March 30, 2017

Magidanci yayi wa 'yan mata 2 fyade

Malam Lawal Zubairu wani dan kasuwa ne a garin Kano da ya gurfana a gaban Kotu akan zargin yi wa wasu tagwayen 'yan mata 2 masu shekara 11 fyade.Karar da aka shigar ranar 18 ga watannan ya biyo bayan kara da mahaifin 'yan matan ya kai ne wa 'yan sanda wanda sanadin hakan yakai ga gurfanar da Malam Zubairu a gaban kotu.

Rufa'i Yunusa dan sanda mai gabatar da kara yayi wa kotu jawabi yadda Lawal Zubairu ya rudi 'yan matan suka bishi zuwa gidan sa inda ya aikata wannan aika aikan.Malam Lawal dai bai amsa laifin sa ba sanadin hakan Alkali ya daga shara'ar zuwa ranar 27 ga watan Afrilu,ya kuma bada umarni cewa a ci gaba da tsare Lawal Zubairu har zuwa lokacin.

@isyakuweb--Ku biyo mu a Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Magidanci yayi wa 'yan mata 2 fyade Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba

Raayin mai karatu

Koma Sama