BBC
Shugaban rikon kwarya na hukumar
EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, Ibrahim
Magu, ya ce wadanda ke tsoron kada a fallasu ne suke yakar sa.
A makon da ya gabata ne dai majalisar dattawan kasar ta ki amincewa da shi a matsayin tabbataccen shugaban hukumar ta EFCC.Kuma wannan shi ne karo na biyu da majalisar ke kin tabbatar da shi.
'Yan majalisar dai na kafa hujja da cewa sun sami rahoto kan Magu daga hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta kasar dake zarginsa.
Rahoton dai ya nuna Ibrahim Magu na da tabon laifi abin da ke sanya shakku kan yiwuwar yakar cin hanci da rashawa.
A wannan hirar da ya yi da Ahmed Abba Abdullahi, Ibrahim Magu ya ce ba haka al'amarin yake ba.
RFI
Wata kotu a kasar Janhuriyar Nijar ta sallami wasu
fararen hula 15 da ake tsare dasu bisa zargin hannu a yunkurin kifar
da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Isufu a shekara ta 2015.
Lauyan mutanen Ali Kadir ya tabbatar da sakin mutann da yake karewa.A watan 12 na shekara ta 2015 ne dai Gwamnatin Muhammadu Isufu ta sanar da cewa ta yi nasarar hana juyin mulki, kuma tana tsare da wasu mutane dake da hannu a ciki.
Majiyoyin samun labarai na cewa an sallami mutane 15, amma kuma akwai manyan sojoji 9 da suka hada da jagoran kifar da Gwamnatin Janar Salou Souleymane wadanda har yanzu ake tsare dasu.
DW
Sama da watanni uku ke'nan kungiyar Boko Haram ke zafafa kai hare-haren kunar bakin kusan kowane mako a wuraren taron jama'a musamman masallatai ko kuma sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri, inda ake samun hasarar rayuka da dukiyoyi da dama. Haka a iya cewa kusan kullum sai jami'an tsaron ko kuma matasa masu ayyukan sa kai na CJFT sun dakile hare-haren kunar bakin wake cikin dare ko da sanyin asubahi wanda yawanci aka fi amfani da mata masu kanan shekaru.
Yachilla Bukar ta Radio Dandak Kura tare da 'yan gudun hijira
Kungoyin
mata sun bayyana damuwa kan yadda ake amfani da mata wasu kanan shekaru
wajen kai hare-haren kunar bakin wake a wannan lokaci. Hajiya Ya Gana
Alkali ita ce shugabar gamayyar kungiyoyin mata ta Najeriya reshen jihar
Borno ta bayyana yadda suke ji da wannan hali da ake fama da shi a
Maiduguri a matsayin wani babban kalubale da ya kamata kowa ya bada
nashi taimako dan ganin masu wannan akidar basu samu nasara ba.Karuwar harin kunar baki wake a birnin Maiduguri dai ya sa al'ummar yin tambayar makasudin dawowar hare-haren bama-baman. gwamnan Jihar Borno kashim Shetima a wata tattaunawa da muka yi da shi ya bayyana cewa abin da ya ke faruwa abin bakin ciki ne kuma gwamnati na daukar matakai don magance matsalar.
Sojojin Najeriya a bakin aiki na tsaro a Maiduguri
Sai
dai duk da irin wadan nan hare-hare da ake kaiwa harkoki na yau da
kullum na ci gaba da gudana, inda mutane ke zuwa kasuwanni da wuraren
ibada ba tare da zullumi ko fargabar wani abu zai same su ba. A wurare
kamar Post Office da Custom da kuma bakin kasuwar Monday Market za a
lura cewa mutane suna sha'anin kasuwancinsu cikin cinkuso kuma babu wasu
matakai na tsaro da a zahiri za'a ce an sa don magance irin hare-haren
da ake kaiwa. VOA
Shugaba kungiyar a jihar Komred Samson Almuru, ya
shedawa taron manema labarai a Yola fadar jihar cewa kungiyar ba ta
anfana ko da sau guda ba daga tallafin da gwamnati tarayya ke rabawa
jihohi.
Ya ce abin takaici shine duk da kasawar da
gwamnati ta yi na ware mata wani kaso na kudin Faris kulob Naira miliyan
tara da ta karba daga gwamnatin tarayya bara don rage bashin da ‘ya’yan
kungiyar ke bin ta.’ko Naira biliyan daya da gwamna Muhammadu Umaru
Jibirilla ya sanar ya ware don rage bashin hakkokin da tsoffin
ma’aikatan ke bi makonni uku da suka gabata, har yanzu ba su gani a kasa
ba’ inji Komred Samson Almuru.
Wadannan kalamai na shugaban kungiyar tsoffin
ma’aikata ta kasa reshen jihar Adamawa ya tada hankalin mukarraban
gwamna Jibirilla dalilin da ya sa kwamishinan kudi na jihar Alh, Sali
Yunusa ya kira taron ‘yan jarida don ya baiwa tsoffin ma’aikata hakuri
da alkawarin zasu biya hakkokinsu da zaran kudin Faris Kulob da shugaba
Buhari ya alkawarta sun samu.
Kawo yanzu, akwai tsoffin ma’aikata da suka share
sama da shekara shida suna yi wa kudaden sallamarsu jiran gawon shanu a
jihar Adamawa.
@isyakuweb--ku biyo mu a Facebook
Tags:
LABARI