• Labaran yau

  March 16, 2017

  Kwallon kafa- Issa Hayatou Ya Sha Kaye a zaben CAF


  Labari da muka samu yanzu-yanzu ya nuna cewa Issa Hayatou ya sha kaye a zaben da aka yi na shugabancin hukumar kwallon kafa na kasashen Africa CAF.Ya sha kaye a hannun Ahmad Ahmad dan asalin kasar Madagascar inda Issa Hayatou ya tashi da kuri'u 20 shi kuma Ahmad Ahmad ya tashi da kuru'u 34.

  Wannan lamarin ya kawo karshen shugabanci na shekara 29 da Mr Hayatou ya share akan karagar shugabancin.Tabbatattun labarai sun shaida cewa daga cikin kasashen da suka goyi bayan zaben Mr.Hayatou ya ci gaba da shugabancin CAF har da Najeriya.

  Isyaku Garba   @isyakuweb .Ku biyo mu a Facebook https://web.facebook.com/isyakuweb 

  AIKO DA LABARI
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kwallon kafa- Issa Hayatou Ya Sha Kaye a zaben CAF Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama