• Labaran yau

  March 03, 2017

  Kebbi,Kakakin Majalisar dokoki ya yanke jiki ya fadi

  Jaridar nigerianeye ta wallafa wani labari a shafin ta na yanar gizo cewa shugaban Majalisan dokoki na jihar Kebbi Hon. Samaila Abdulmumin ya yanke jiki ya fadi ranar Laraba 2/3/2017 da yamma a yayin da suke cikin duba wata kwangilar aikin hanya a garin Ribah da ke karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi.

  Gwamna Atiku Bagudu ya gaiyaci Kakakin Majalisar dokoki na jihar Kebbi ne domin ya kasance a cikin tawagar sa zuwa wajen duba aikin.Jaridar ta kara da cewa bayan aukuwan lamarin,wasu jami'an tsaro sun garzaya da Kakakin zuwa Birnin kebbi a cikin wata motar daukan marasa lafiya da ba'a yi mata wani shaida ba.

  A cewar jaridar,har ya zuwa lokacin da aka buga rahotun,ba a san takamammen rashin lafiyar da ke damun Kakakin Majalisan ba.Kuma kokarin da suka yi domin su sami bayani a takwarorin sa 'yan Majalisan dokoki na jihar Kebbi ya ci tura domin babu wanda yace da su uffan.

  Isyaku Garba - Birnin kebbi
  @isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi,Kakakin Majalisar dokoki ya yanke jiki ya fadi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama