• Labaran yau

  March 15, 2017

  Kebbi-Gwamnati ta fara sayar da takin zamani akan N5,500


  Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya kaddamar da shirin sayar da takin zamani na 2017 a garin Jega inda ya bayyana cewa Gwamnatin sa ta samar da tonn 100,000 domin sayarwa manoma a jihar.Ya ce za'a sayar da takin zamanin akan N5,500 a kan buhu daya ga manoma saboda bunkasa harkar noman rani a jihar.Shirin sayar da takin zai ci gaba a duk kananan hukumomi 21 da ke cikin jihar Kebbi.

  Ya kuma kara da cewa wannan ya biyo bayan yarjejeniya ta fahimta tsakanin kasar Morocco da Gwamnatin jihar kebbi domin a samar da wadataccen takin zamani akalla tonn miliyan1.Gwamnan ya kuma yi kira ga manoman da suka karbi bashin Gwamnati a can baya cewa su biya bashin domin wadanda basu sami bashin ba suma su amfana da kudin.

  Alh.Atiku Bagudu ya sanar da alkawarin taimakon Naira Miliyan 20 ga wani injiniya mai gyara dan shekara 20 Bello Umar a Jega domin ya bunkasa hazakarshi domin amfanin jihar Kebbi nan gaba.Ya kara da cewa za'a sa wannan yaron cikin kwamitin masu kere kere a karkashin kulawar mataimakin Gwamnan jihar kebbi Col.Samaila Yombe.

  Isyaku Garba   @isyakuweb .Ku biyo mu a Facebook https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi-Gwamnati ta fara sayar da takin zamani akan N5,500 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama