• Labaran yau

  March 29, 2017

  Kauyen Tarasa Birnin kebbi: 'Yan Mata 5 sun mutu a cikin ruwa

  Wasu 'yan mata su biyar 'yan shekaru 10 zuwa 15 a Unguwar Kaye na Kauyen Tarasa a karamar hukumar Birnin kebbi sun gamu da ajalinsu ranar Talata a yayin da suka nutse a cikin Tafkin Madobiya da aka fi sani da ruwan 'yan Indiya (Indian water) wanda hakan yayi sanadin rasuwar su.

  'Yan matan sun je tafkin ne domin suyi iyo bayan sun gama dibar kayan miya domin amfani girki a gida,amma da yake tsautsayi da kuma ajali yayi kira sai suka je domin su yi iyo.Kamfanin dillancin labarai ta Najeriya ta kara da cewa Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe ya jagoranci wata tawaga ta Gwamnati inda suka yi ta'aziyya wa iyalan mamatan.


  @isyakuweb--Shafin mu na Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kauyen Tarasa Birnin kebbi: 'Yan Mata 5 sun mutu a cikin ruwa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama