• Labaran yau

  March 05, 2017

  Hukumar ayyukan asiri da tsaro ta DSS ta kama wadanda ake zargi da kashe Sheikh Albani


  Sashen ayyukan leken asiri da ayyuka na musamman ta Hukumar DSS da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ta damke mutane 7 wanda take zargi da cewa sune 'yan kungiyar Boko Haram wanda suka kashe shahararren malamin addinin nan a Zariya, Sheikh Auwal Adam Albani , a yayin da yake tuka mota tare da matarsa da yaronsa yayinda yake hanyan dawowa daga karatu a makarantan cibiyar Markaz Salafiyya da ke Tudun wada Zariya a ranan 1 ga watan Fabrairu, 2014.Idan baku manta ba,bayan sun kashe shi rahotanni sun nuna cewa sanda suka ja gawar shi a kasa.

  Wannan danyen aikin ya hadu da la'anta ta Malamai da al'umma Musulmi akan wadanda suka aikata wannan abin a kan wannan bawan Allah,wanda har gobe duniyar Musulmi ba za ta iya mancewa da kokarin da ya yi wa Musulunci ba,musamman lakcocin da yake bayar wa da kuma litattafai da ya wallafa domin Musulunci.

  Isyaku Garba
  @isyakuweb   KU BIYO MU A FACEBOOK


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hukumar ayyukan asiri da tsaro ta DSS ta kama wadanda ake zargi da kashe Sheikh Albani Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama