• Labaran yau

  March 15, 2017

  Hukumar Kwastam ta dakatar da kudurin ta kan harajin tsofaffin motocin tokumbo

  Hukumar hana fatakwauri ta Kwastan ta dakatar  da kudurinta na karbar kudin fito na duti akan motoci da aka shigo da su kasannan da aka fi sani da suna tokumbo.Wannan labarin ya bayyana ne sakamakon ziyarar bazata da shugaban kwastam na kasa Hamid Ali ya kai a ofishin shugaban majalisar dattawa da yammacin jiya Talata inda akayi tattaunawar sirri a tsakanin shugabannin biyu.


  Hukumar kwastam ta yi barazanar sa kafan wando daya da duk mai mota tokumbo da bai biya harajin duti ba .Amma a waje daya Majalisar Dattawa ta Najeriya ta bukaci shugaban hukumar ta kwastam ya bayyana a gabanta domin ya kare wannan kudurin da yake nufin aiwatarwa wanda Majalisar tace zai haifar da matukar matsi da wahala a kan talakan Najeriya.

  Sai dai majiyarmu ta tabbatar mana da cewa a yanzu haka an dakatar da wannan kudurin kuma ba zancen sanya shinge a manyan hanyoyi domin binciken motocin da ake zaton tokumbo ne a Najeriya wanda ake zaton hukumar kwastam zata yi.

  Isyaku Garba
  Ku biyo mu a Facebook https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hukumar Kwastam ta dakatar da kudurin ta kan harajin tsofaffin motocin tokumbo Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama