• Labaran yau

  March 15, 2017

  Gwamnatin jihar Kogi ta rushe gidan wani mai satan Mutane  A yau dinnan Gwamnatin jihar Kogi ta bayar da umarni domin a rushe wani gida mai hawa daya mallakin shahararren mai satan mutanennan mai suna Alh.Tijjani Bakare bayan yayi ikirarin cewa shine madugun masu satan mutane a cikin jihar Kogi.


  A yayin da hukumar 'yan sanda ta jihar Kogi ta kamashi,Bakare ya gaya wa 'yan sandan cewa shine ke jagorancin kungiyoyin da ke sace mutane domin yin garkuwa da su ta hanyar neman kudin diyya.Rahotanni sun nuna cewa an sami bindigogi,albarussai da ababen fashewa masu illa a gidanshi a yayin da 'yan sanda suka bincike gidan

  Rushe wannan gidan ya samo asali ne akan wata doka ta ta'addanci da majalisar dokoki ta jihar Kogi ta gabatar kuma tsohon Gwamnan jihar Kogi Idris Wada ya sanya wa hannu a zaman doka.


  Isyaku Garba
  @isyakuweb  Kubiyo mu a Facebook https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamnatin jihar Kogi ta rushe gidan wani mai satan Mutane Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama