• Labaran yau

  March 03, 2017

  Gwamna Atiku ya ba da Kwangilar yin Hanyoyi a Masarautar Zuru

  Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya ba da kwangilar aikin titi a Masarautar Zuru,ayyukan da ya kaddamar da fara aikin su ya hada da hanyar Riba zuwa Maga,Riba zuwa Wasagu  har zuwa Bena,haka kuma hanyar da ta taso daga garin Dabai zuwa Amanawa ta cikin garin Zuru.Gwamna Atiku ya ce wannan wani mataki ne na fara cika alkawari da ya yi a lokacin yakin neman zabe.

  Gwamnan ya kuma ce Gwamnatin sa tana kokari akan ganin cewa Masarautar Zuru ta wadata da wutan Lantarki.Ya ce a yanzu haka an cire Bagudo, Ka'oje da Koko-Besse daga layin wutan Lantarki na Yelwa Yauri domin a inganta wutar lantarki ta Zuru.Majiyar mu ta ce haka zalika Gwamnatin Atiku Bagudu ta bayar da kwangilar gyara itatuwa da wayan mutan lantarki da ta dauko wutar daga Yauri zuwa Zuru.

  Isyaku Garba
  @isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamna Atiku ya ba da Kwangilar yin Hanyoyi a Masarautar Zuru Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama