• Labaran yau

  March 20, 2017

  Dalibai Inyamirai sun yi mubaya'a ga kasancewar Najeriya kasa daya

  A yau dinnan dubu dubatan dalibai 'yan asalin kabilar inyamirai (Igbo) karkashin sahen dalibai na kungiyar Inyamirai na ohanaze ndi igbo suka aiwatar da zanga zangar lumana domin su nuna mubaya'ar su ga kasancewa Najeriya kasa daya su kuma tabbatar wa gwamnatin Najeriya goyon baya.Daliban sun zagaya titunan birnin Abuja har izuwa fadar shugaban kasa ta dutsen Aso.


  A yayin da yake wa masu zanga zangan jawabi a dandalin hadin kai na kasa a Abuja, shugaban sashen dalibai na kungiyar Inyamirai ta ohanaze ndi igbo comared  Osisioma Osikenyi Igwe yace "al'umman Inyamirai sun yi mummunar kuskure a can baya,a yanzu kuwa basa son su sake maimaita irin wannan kuskuren"

  Ya kuma bukaci al'umman kudancin Najeriya masu tada kayan baya da cewa su rungumi zaman lafiya,ya kuma roki gafara ga jam'iyyar APC da kuma gwamnatin Buhari saboda barazana da kungiyoyin Inyamirai masu tada kayan baya kamar IPOB da MOSSOB suka yi.

  @isyakuweb - Ku biya mu a Facebook
  http://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dalibai Inyamirai sun yi mubaya'a ga kasancewar Najeriya kasa daya Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama