Dalibai 4 sun mutu a Makarantar sakandare ta Fana a karamar hukumar Suru

Dalibai hudu a Makarantar sakandare da ke garin Fana a karamar hukumar mulki ta Suru da ke jihar Kebbi sun mutu a sakamakon bullar cutar gudanawa da kumburin ciki,kamfanin dillancin labarai ta Najeriya (NAN) ta ce an kuma garzaya zuwa Asibiti da sauran dalibai guda bakwai da suka kamu da cutar inda suke samun kulawa a babban Asibitin garin Kamba da ke karamar hukumar Dandi.Sakataren watsa labarai na Gwamnati Alh.Abubakar Mu'azu ya gaya wa kamfanin dillancin labarai ta Najeriya cewa mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya jagoranci wata babbar tawaga da ta kai ziyarar ta'aziya ga shugabannin Makarantar.

Alh.Mu'azu yace cikin tawagar da suka je wajen wannan ta'aziyyar harma  da Kakakin  Majalisar Dokoki ta jihar Kebbi Hon. Alh. Abdulmumini Kamba ,tawagar ta ziyarci daliban su bakwai da aka kwantar a Asibiti kuma Gwamna Atiku Babugu ya bayar da umarni akan cewa a samar da ruwan sha mai tsabta da kuma abubuwan da suka dace na inganta tsabta da kuma lafiyar dalibai a Makarantar.

Isyaku Garba

@isyakuweb  Ku biyo mu a facebook
Dalibai 4 sun mutu a Makarantar sakandare ta Fana a karamar hukumar Suru Dalibai 4 sun mutu a Makarantar sakandare ta Fana a karamar hukumar Suru Reviewed by on March 07, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.