Buhari ya dawo Nigeria bayan doguwar jinya



Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gida bayan shafe mako takwas yana jinya a birnin London na ƙasar Ingila.
Shugaban ya sauka a wani filin jirgin sama na Kaduna, inda manyan jami'an gwamnatin jihar da kuma na tarayya suka tarbe shi.
Tun a ranar Talata 19 ga watan Janairu ne Shugaba Buhari ya tafi hutu da kuma ganin likita.
Daga bisani ya tsawaita hutun nasa, saboda abin da fadarsa ta ce, umurni ne na likitansa, domin yi masa gwaje gwaje da kuma buƙatar kara hutawa.
Hutun jinyar da kuma tsawaita shi da shugaban ya yi, sun janyo muhawara sosai a tsakanin 'yan kasar.
Har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ke damun shugaban Muhammadu Buhari amma jami'ansa sun nace cewa babu wani abin damuwa a cikin lamarin.
A ranar Alhamis ce mai magana da yawun shugaban Femi Adeshina ya sanar da cewa Muhammadu Buhari zai koma gida.
Sanarwar da ya fitar ta ce shugaban ya gode wa É—aukacin al'ummar Nijeriya da ma na kasashen waje kan addu'o'in da suka rika yi masa da fatan alkhairi.
A baya-bayan nan wayar da ya yi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, lokacin da aka fara jin muryarsa tun bayan zuwa hutun jinyar, ya sa zuciyar 'yan ƙasar da dama kwanciya.
An yi ta ganin hotunan Muhammadu Buhari da wasu fitattun 'yan Nijeriya yayin ziyarar da suka riƙa kai masa lokacin da yake jinya a London.
BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN