• Labaran yau

  March 14, 2017

  Boko Haram ta yanka "yan leken asiri" guda 3

  Boko Haram ta fito da wani bidiyo wanda Sahara Reporters ta samu a ciki an nuna wasu mutane uku a tsugune a yayin da wasu 'yan kungiyar BH da suke rufe da fuskokin suke tsaye a bayansu.A cewar Sahara Reporters bangaren Abubakar Shikau ne suka samar da hoton bidiyon.Wanda daga karshe aka nuna yadda aka yanka wadannan mutanen guda uku.


  Rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta BH ta ce mutanen guda uku munafukai ne 'yan leken asiri wanda hukumar leken asiri ta soja (DMI) ta turo su domin suyi mata leken asiri akan ayyukan kungiyar ta BH.Hoton bidiyon wanda aka nada shi a harsunan Hausa da Larabci ya nuna wasu shugabanni kamar su Shugaba Muhammadu Buhari,Donald Trump na Amurka,tsohon shugaban Amurka Barack Obama da sauran shugabannin kasashen turai duka anyi maganarsu a cikin hoton bidiyon na tsawon minti 7.

  Kungiyar ta Boko Haram ta nuna jerin wasu tarin makamai wanda a ciki har da bindigogin roka ta harbin jiragen sama,kuma a cikin hoton bidiyon tayi barazanar cewa tana rike da babban yanki wanda har yanzu sojin Najeriya suka kasa kamawa.

  @isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  AIKO DA LABARI 


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Boko Haram ta yanka "yan leken asiri" guda 3 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama