• Labaran yau

  March 22, 2017

  Bama bamai 3 sun tashi a Maiduguri da safiyar yau


  An sami tashin tagwayen bama bamai har guda uku da sanyin Asubahin yau a kusa da tashar mota ta Muna da ke cikin garin Maiduguri wanda yayi sanadiyar jikata mutane 18 yayin da mutane 4 suka mutu.

  A zantawa da yayi game da lamarin ga manema labarai Kwamishinan 'yan sanda na jihar Barno Mr.Domian Chukwu ya tabbatar da tashin bama baman da misalin 4:30 na safiyar yau 22 ,Maris, 2017.

  Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin tada bama baman.Wannan irin lamarin ya zama ruwan dare a wannan yankin na Najeriya inda tashin bama bamai ya zama abin da mazauna yankin ke gani daga lokaci zuwa lokaci.

  @isyakuweb - Ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bama bamai 3 sun tashi a Maiduguri da safiyar yau Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama