An tashi 1-1 wasan kwallo tsakanin Lion Stars da M/Gandu Villa a Birnin kebbi

A yammacin yau Asabar aka buga wasan kwallon kafa tsakanin Kulab na kwallon kafa ta Lion Stars da Makerar Gandu Villa (Villa Real) a babban filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin Kebbi.Wadannan kungiyoyin suna daga cikin kungiyoyin kwallon kafa da ke tashe a cikin garin Birnin kebbi.

'Yan wasan kungiyoyin biyu  sun nuna kwarewa da jajircewa domin ganin kowane bangare ya zura kwallaye a ragar abokin wasansa.

Dan wasa Falsa daga Makerar Gandu Villa (Villa Real) shi ya fara zura kwallo a ragar Lion Stars,sa'annan aka ci gaba da wasa.Daga bisani Hassan Lauran daga Lion Stars shima ya rama ta hanyar zura kwallo a ragar Makerar Gandu villa.

Masud Muhammed Nata'ala Mataimakin sakataren kungiyar kananan 'yan wasan kwallo na jihar Kebbi ya yi bayani cewa kwamitin sun shirya wadannan wasanni ne domin su nishadantar,kuma su kayatar da jama'a masu kallo.

Kalli bidiyo a kasa


@isyakuweb--Ku biyo mu a Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb


An tashi 1-1 wasan kwallo tsakanin Lion Stars da M/Gandu Villa a Birnin kebbi An tashi 1-1 wasan kwallo tsakanin Lion Stars da M/Gandu Villa  a Birnin kebbi Reviewed by on March 25, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.