• Labaran yau

  An kama 'yan Boko Haram a Ekiti

  Hukumomin tsaro sun ce sun kama wani dan kungiyar Boko Haram a jihar Ekiti.


  A wata sanarwa da babban jami’in hukumar tsaro ta farin kaya DSS Tony Opuiyo ya fitar, ya ce jami’an su sun kai farmaki a sassa daban-daban na Nijeriya, inda su ka kama ‘yan ta’adda da masu son tada zaune tsaye da dama.

  Ya kara da cewa, a ranar Litinin da ta gabata ne, hadin gwiwar rundujar soji da ta DSS ta kama mutumin da ake zargin dan Boko Haram ne mai suna Adenoyi Abdulsalam a birnin Ado Ekiti.

  A cewar sa, kafin a kama Abdulsalam, an kai farmaki a kan mayakan Boko Haram da dama a arewacin Nijeriya, wadanda su ka hada da jihohin Bauchi, da Yobe, da Gombe, da Nasarawa, da Kaduna da kuma Kogi.

  Opuiyo ya kara da cewa, a cikin wadanda aka kama har da wani dan Boko Haram mai suna Usman Ladan Rawa, wanda ake yi wa lakabi da Mr X a Lafia ta jihar Nasarawa.

  Haka kuma, an kama wani dan Boko Haram mai suna Nasiru Sani, wanda ake yi wa lakabi da Osama a Bauchi, yayin da aka kama wani dan Boko Haram mai suna Adamu Jibrin.  (Liberty)@isyakuweb--Ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kama 'yan Boko Haram a Ekiti Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama