• Labaran yau

  March 21, 2017

  An gano gawar Likita da ya kashe kanshi bayan ya tsunduma a cikin teku

  A 'yan kwanakin da suka wuce ne wani likita Allwell Oji  ya tuko motarshi zuwa gadar Mainland ta 3 da ke cikin garin Lagos,rahotanni sun ce bayan isowarshi sai ya tsayar da motar,ya fito sai kawai ya fada cikin teku wanda hakan ake kyautata zaton cewa yayi sanadin mutuwarshi a cikin ruwan.


  'Yan sanda masu kula da gabar ruwa na birnin Lagos sun yi ta naiman gawan likitar wanda a yau aka ga wata gawar wanda ake kyautata zaton cewa gawar likitar ce.

  Jaridar thenationonline ta wallafa cewa 'yan sanda sun kira Mahaifiyar mamacin da iyalinsa domin su shaida gawar ko ta likitan ne.Jaridar ta ce a cewar 'yan sandan bazasu iya gane kai tsaye ko shi ne ake nema ba domin basu da hoton likita kafi faruwar lamarin.

  @isyakuweb - Kubiyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An gano gawar Likita da ya kashe kanshi bayan ya tsunduma a cikin teku Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama