• Labaran yau

  March 18, 2017

  An fara taron karawa juna ilimi mai taken "gina kasa ta hanyar dogaro da kai" a Birnin kebbi


  A yanzu haka an fara gudanar da taron karawa juna ilini na lakca wanda hadaddiyar kungiyar Limamai da Malamai ta jihar Kebbi karkashin jagorancin Alh.Ibrahim Bayawa suka shirya wanda ake gudanarwa yanzu haka a dakin taro na sansanin Alhazai da ke hannun riga da Asibitin tarayya (Federal medical center) a garin Birnin kebbi.

  Taron lakcan wanda ake sa ran za'a kammala shi a gobe yana dauke da taken "gina kasa ta hanyar dogaro da kai" kuma tuni masana akan bangarorin ilimi da rayuwa suka fara gabatar da jawabai na lakca ga mahalarta taron.

  @isyakuweb - Ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An fara taron karawa juna ilimi mai taken "gina kasa ta hanyar dogaro da kai" a Birnin kebbi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama