• Labaran yau

  March 08, 2017

  A daina bata sunan Malamai akan Addu'a don Buhari a Birnin kebbi
  A wata badakala ta rashin gaskiya da fahimtar al’amari da ya danganci labari dangane da kudi naira miliyan biyu da ake zaton mai girma Gwamnan jihar Kebbi ya bayar wa wa’yanda suka tsara Addu’ar da aka yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda Malamai suka jagoranci  addu’ar a babban Masallacin Idi da ke Unguwar Gesse da ke cikin garin Birnin kebbi ranar Juma’a 24/2/2017,labari ya baiyana a shafin sada zumunta na Facebook wai Malamai suna fada akan Naira Miliyan daya da Gwamnatin jihar Kebbi ta bayar domin su raba a matsayin sadaka.Sakamakon binciken da ISYAKU.COM ta gudanar ya nuna cewa gaskiyar al’amarin shine ba wani rigima ko fada a tsakanin Malamai akan zancen kudin domin babu wanda ya ba ko wane Malami ko sisi,babu yanda zaka yi fada akan abin da baka gani ba.

  ISYAKU.COM ta kaddamar da bincike domin tantance sahihancin zarge zarge akan ko Malamai sun karbi kudi a matsayin sadaka dangane da wannan Addu’ar da aka aiwatar ranar Juma’a 24/2/2017 ?...amsar wannan tambaya shi ne BABU.A nashi bayanin a yayin da yake zantawa da ISYAKU.COM  Malam Bashar Jabbo wanda daya ne daga cikin wadanda suka wakilci kungiyar Jama’atu Ta’awanu Alal Birri Wattaqawa ta jihar Kebbi a wajen wannan Addu’ar yayi bayani akan cewa su kam basu gan ko sisi ba kuma idan har gaskiya ne Gwamnati ta bayar da Sadakar kudi ko wani abu a ba Malamai,to yana da kyau a ce sakon ya iso ta hannun wakilin Malamai domin a raba sadakar a bisa adalci.

  A ci gaba da tantance gaskiya ISYAKU.COM ta gano cewa ko motar da aka yi amfani da ita wanda kuma na’urar daukaka Magana ta motar ce watau laspika aka yi amfani da su  a wajen taron Addu’ar amma duk da haka ba’a ba mai motar ka sisi ba.Motar dai an ce mallakin Malam Abubakar Izala kaset ne,wanda kuma wakili ne daga cikin wakilan Izala JIBWIS a wajen wannan taron Addu’ar.

  SHARHI

  ISYAKU.COM tana kira ga Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu akan cewa,yana da kyau Gwamnati ta juyo wajen wannan zancen wanda tuni ya zama ruwan dare gama Duniya a shafukan sada zumunta na Facebook,Twitter da sauran su.Ba kasawa bane a kira taron Malamai zalla a gidan Gwamnati ko aike na sako domin a yi masu bayani akan cewa kudin da ake zaton an bayar ba wai domin Malamai ne aka bayar da kudin ba domin haka zai kawar da zarge zarge a cikin sha’anin.

  Ta yin la’akari da gudunmuwa da Malamai suka bayar a wajen wannan Addu’ar gaskiya a tunanin ISYAKU.COM bai dace ace wai irin wannan kananan maganganu suna tasowa ba kuma babu wanda ya ce kala,amma da wasu daga cikin Malaman suka dinga sako Addu’a ai wasu har zarcewa suka yi da kuka.  Isyaku Garba - Birnin kebbi
  @isyakuweb   KU BIYO MU A FACEBOOK
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: A daina bata sunan Malamai akan Addu'a don Buhari a Birnin kebbi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama