Za a hana talaka futuk auren mata barkatai — Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce majalisarsa tana shirye-shiryen samar da wata doka da za ta hana mazan da basu d...

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce majalisarsa tana shirye-shiryen samar da wata doka da za ta hana mazan da basu da karfi auren mata fiye da daya a jihar.
Sarki Sunusi ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taro a Abuja na tunawa da marigayi Ambasada Isa Wali, wanda ya mutu shekaru 50 da suka wuce.
Ya ce yawan aure-aure da mutane ke yi alhalin basu da karfin rike iyali kamar yadda shari'ar Musulunci ta tanada, yana matukar yin mummunan tasiri wajen tarbiyyar yara da basu ilimin da ya dace.
Hakan a cewarsa saboda yadda talauci ke dabaibaye iyayensu ga rashin basu kulawar da ta kamata yasa mafiya yawa daga cikin irin wadannan yara na karewa ne a mastayin 'yan daba ko 'yan ta'adda.
Sarkin ya ce zai tabbatar da cewa dokar ta bi dukkanin hanyoyin da suka dace domin gwamnatin jihar ta Kano ta tabbatar da ita.
Mai martaba ya yi nuni da cewa abin takaici ne yadda za a ga mutum yana fama da cin yau da na gobe, amma zai auri mace fiye da daya, ya kuma haifi 'ya'ya masu yawan da ba zai iya ciyar da su ba, ko tufatar da su, ko samar musu da isasshen muhalli ba, ballantana ya basu irin tarbiyyar da al'umma za ta yi alfahari da su.
Ya ce mutane suna fassara damar da Musulunci ya bayar na auren mace fiye da daya ba daidai ba.
Kuma a yawancin lokuta ba tare da sun cika sharuddan da addini ya tanada ba na kara auren.
Dama tun kusan shekara daya da ta gabata ne, Sarkin ya kafa kwamitin malaman don yin nazari tare da tsara yadda dokar za kasance kafin gabatar da ita a gaban majalisar dokokin jihar.

BBC

COMMENTS

VISITOR
Name

AL-AJABI,22,BIRNIN-KEBBI,21,DUNIYA,19,FADAKARWA,22,FASAHA,3,HOTUNA,34,LABARI,351,NISHADI,49,SANARWA,13,SHARHI,8,SIYASA,15,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Za a hana talaka futuk auren mata barkatai — Sarkin Kano
Za a hana talaka futuk auren mata barkatai — Sarkin Kano
https://1.bp.blogspot.com/-6SuiHbuksbw/WKsiUkEpNzI/AAAAAAAADC0/DISlcxGfT-UVPglpyzxDB9wuVH9_72brQCLcB/s320/E.jpg
https://1.bp.blogspot.com/-6SuiHbuksbw/WKsiUkEpNzI/AAAAAAAADC0/DISlcxGfT-UVPglpyzxDB9wuVH9_72brQCLcB/s72-c/E.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/02/za-hana-talaka-futuk-auren-mata.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/02/za-hana-talaka-futuk-auren-mata.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All WASU KARIN LABARAI LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy