Yiwuwar amfani da Dabbobi wajen kera Jiragen sama masu tuka kan su


Masana ilimin fasahar kere-kere na duba yiwuwar hanyar da za su yi amfani da kwari don kera jiragen sama masu tuka kawunansu da ake amfani da su wajen leken asiri da samar da tsaro da ake kira da a turance da Air Drones.
Shi wannan aikin(project) ana kiran sa da suna Idon-Mazari (dragonfleye) wanda ke amfani da wani kira da a ke cewa optogenetic.
Wannan wani tsari ne wanda ma su nazarin halittu ke amfani da haske wajen sarrafa kwayar hallita.  Masu bincike sun canza kwayoyin hallitan mazari yadda zai rinka amfani da haske don yin hakan zai ba masana kimiyyar samun sauki wajen ba kwaron umurnin da su ke so.
A karin bayani, injiniyoyi sun harhadawa mazari mitsitsin jakar-baya wanda zai hada naurar kwakwalwa dabban da ke kula da tashin sa da nakuran kwamfuta. Yin hakan zai taimaka ma su wajen kula da kuma ba dabban umurnin da su ke so a yayin da yake sama a nisa kan iska.
Wannan aikin aikatayya ne tsakanin dakin binkin Charles Stark Draper wadanda su ka hadda jakar-bayan da ke ba mazari umurni, da kuma Asibitin Howard Hughes wadanda suka gano sannan kuma su ke bincike game da yanda za’a tuka ita wannan jakar bayan an daura ma kwaron a baya.   A karshe dai, Masana suna cewa wannan fasahan za’a iya amfani da ita wajen kara bun kasa ilimin maganin mutum musamman wajen kera metsisin nakurorin bincike na asibitoci, da kuma samun amintaccen dama wajen yin aiki da naurar kwakwalwa ta mutum a ilmin likita.
MUJALLARMU

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN