Yadda ake Amfani da Ganyen Goba Wajen Kara Tsawon Gashi

A maimakon badda makudan kudade wajen sayen mayukan kara gashi da hana zubewar shi, za’a iya amfani da ganyen gwava wanda bincike ya nuna cewa ya fi karfi da inganci akan yawancin kayan gyaran gashin da ake sayarwa na kamfani.
Ganyen gwava na dauke da sinadaran da ke kara yawan gashi, ya tsaida zubar shi, ya kuma kara mashi lafiya da sheki.
Za’a dafa ganyen gwava kamar cikin hannu ko damka daya a cikin lita daya na ruwa, sai a barshi ya tafasa na tsahon minti 20, sannan sai a sauke a barshi ya huce. Idan ya huce za’a matse ganyen a tace ruwan. Wannan ruwa shi za’a mursuka cikin gashin tun daga kasa.Ko dai a mursuka ruwan bayan an wanke gashi a barshi na tsahon awanni sannan a wanke, ko kuma a mursuka shi da daddare, a rufe da hular leda a kwana da shi.
Idan aka ci gaba da amfani da Ganyen gwava, za’a ga banbanci. Gashi zai kara laushi, ya karfafa, sannan ya daina zuba, al’amarin da zai sa shi ya kara tsaho cikin dan kankanin lokaci.
ALUMMATA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN