Tsoffin ‘Yan Sanda a Jahar Jigawa Sun Tsunduma Bara

Kimanin tsofaffin ‘yan sanda 22 ne suka tsunduma bara a jahar Jigawa a sakamakon kwashe watanni 17 da suka yi da yin ritaya ba tare da an...

Kimanin tsofaffin ‘yan sanda 22 ne suka tsunduma bara a jahar Jigawa a sakamakon kwashe watanni 17 da suka yi da yin ritaya ba tare da an biyansu hakkokinsu na giratuti da fansho ba.
A wani rahoto da jaridar Leadershi Hausa ta wallafa, ta bayyana cewa an yi watsi da wadannan tsoffin ‘yan sanda, ba tare da la’akari da shekaru 35 din da suka yi suna bautawa kasa ba, al’amarin da ya sa suka shiga halin kaka-ni-kayi.
An zanta da wasu daga cikin mutanen kamar su Insifekta Abubakar Muhammed wanda ya bayyana cewa dole ce ta sanya cikin yanayin bara domin neman abinda zai ci tare da biyan kudin hayar gidan da suke zaune.
Sai wani tsohon dan sanda mai suna Baba Musa wanda ya ce “dole in yi bara domin a halin yanzu an kori yarana daga makaranta su kimanin shida duk da cewar ba mu da abin da za mu ci.”
Haka shima wani wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce “wallahi a halin yanzu tuni maigidan da nake zaune a ciki ya kori iyalina daga cikin gidan sakamakon gaza biyan kudin haya wadda hakan dole ya jefa ni cikin barace-barace domin karfinmu ya kare babu wadda zai dauke mu wani aiki”
Tsoffin ‘yan sandan sun ce duk wani yunkurinsu na neman hakkin su daga hukumar ‘yan sanda da kuma kamfanin da ke da hakkin biyan su kudaden ya ci tura.
An nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jahar, SP Abdul Jinjiri ta wayar salula, inda ya bukaci a bashi lokaci ya yi bincike akan al’amarin. Sai dai har lokacin da aka wallafar rahotan ba a ji daga gare shi ba.
MUJALLARMU

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,25,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,39,JAKAR MAGORI,18,LABARI,416,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Tsoffin ‘Yan Sanda a Jahar Jigawa Sun Tsunduma Bara
Tsoffin ‘Yan Sanda a Jahar Jigawa Sun Tsunduma Bara
https://2.bp.blogspot.com/-mO9jMsODUK0/WJTIgMyCfbI/AAAAAAAAChQ/Pb7AIiOzmoQjSHlEdQjvLKjp4tmGaUmCgCLcB/s320/Beggars-1.jpg
https://2.bp.blogspot.com/-mO9jMsODUK0/WJTIgMyCfbI/AAAAAAAAChQ/Pb7AIiOzmoQjSHlEdQjvLKjp4tmGaUmCgCLcB/s72-c/Beggars-1.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/02/tsoffin-yan-sanda-jahar-jigawa-sun.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/02/tsoffin-yan-sanda-jahar-jigawa-sun.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy