Nigeria: Kotu ta yanke wa soja hukuncin yarin shekara 7


Kotun musamman ta rundunar sojin Najeriya da ke zamanta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta yanke wa wani sojan kasar zaman gida yari na shekara 7, bisa samunsa da laifin kisa ba da niyya ba.
Sojan wanda ba a bayyana sunansa kotun ta musamman ta same shi da laifin harbe wani mutum ,mai suna Umar Alkali a kasuwar Monday Karket da ke Maiduguri a ranar 23 ga watan Disamba na shekara ta 2015.
Kotun ta ki amincewa da hujjar da sojan ya gabatar ta cewa ya harbi mutumin ne a kokarin kare kansa.
Inda ya ce mutumin ya yi kokarin kwace bindigarsa ne, wanda a kan haka ne shi kuma ya harbe mutumin.
A sanarwara da kakakin rundunar sojin Birgediya Janar sani Usman Kuka-sheka ya bayar mai dauke da bayanin, ya kuma ce kotun, wadda ke karkashin shugabancin Birgediya Janar Olusegun Adeniyi, ta kuma sami wani sojan da laifin guje wa aikin soji, wanda ta yanke masa hukuncin daurin wata 14.
BBCHausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN