Matasan Tsohon Garin Birnin Kebbi sun fi kwazo wajen neman abin hannu

Sakamakon wani bincike da na gudanar na tsawon watanni Uku a Garin Birnn kebbi ya nuna cewa Matasa da suka fito daga tsohon garin Birnn kebbi sun fi nuna jajircewa da hakuri wajen neman abin hannun su sabanin takwarorin su da ke wasu anguwanni a cikin garin Birnin kebbi.
Matasan na tsohon gari na da hakuri wajen yin kananan sana'oi,kamar sana'ar tireda,okada (kabu-kabu) tuka vespa (keke-napep) aiki gini,penti kai har da sana'ar sayar da Lemu ko kayan marmari da sauran su. Ta yin hakan ya kawo karuwar kudin shiga sosai a hannu wadannan matasan.Bugu da kari sana'ar na duke tsohon ciniki watau noma,sana'a ce da rinjayen matasan ke yi,galibi sabo da jagorancin Iyayen su maza wajen tafiyar da ayyukan gona.
Bayan tsohon gari a wannan tsari na dogaro da kai ga Matasa,sai Tudun wada da Makerar Gandu,inda su ma binciken ya nuna sun rungumi sana'ar noma musamman na shinkafa sosai.A sanin kowa ne dai cewa,mafi rinjayen kananan sana'oi galibi matasa da suka fito daga kauyukka na kewaye da garin Birnin kebbi ne ke shigowa su yi su a nan Birnin Kebbi,amma yanzu lamari ya canja.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN