Birnin kebbi- Kotu ta daure "dan iska" wata 8, ko taran N15,000

A ci gaba da labari da muke dauko maku daga ranar farkon faruwar wani al'amari da ya shafi wani matashi dan asalin jihar Sokoto mai suna Hamisu Abubakar,wanda yayi yunkurin yin "iskanci" da wani karamin yaro ranar 12/2/2017 a Nassarawa 2 na garin Birnin kebbi,kuma lamarin da ya kai ga jami'an 'yan sanda wanda suka gurfanar da shi Hamisu gaban Alkalin Kotu ta Sharia ta Nassarawa 1 ta hannun mai gabatar da kara na 'yan sanda Kofur Faruku ranar 15/2/2017.

Idan baku manta ba,bayan Kofur Faruku ya karanta wa Hamisu Abubakar laifin da ake tuhumar sa da aikatawa,Hamisu bai yi jayayya ba a gaban Alkali Alh.Mu'awiyya,a bisa wannan dalilin ne Alkali Mu'awiyya ya bukaci a dawo yau Laraba 22/2/2017 domin ya yanke hukunci.Da misalin 1:24 Alkali Alh.Mu'awiyya ya karanta sashen doka da ta yi bayanin tanadi da hukuncin irin laifin da Hamisu ya yi yunkurin aikatawa.Daga bisani Alkalin ya tambayi Hamisu ko yana da wani abun da zai ce wa Kotu? shi kuma Hamisu ya ce eh,sai Hamisu ya roki Kotu ta yi masa sassauci.

Bayan jawabin na Hamisu,Alkali ya tambayi mai gabatar da kara na 'yan sanda Kofur Faruku ko wanda ake karan ya taba aikata irin wannan laifin? shi kuma yace a ah.A bisa wannan dalili Alkali ya tambayi Hamisu ko yana zuwa Makaranta? shi kuma Hamisu ya amsa cewa eh.Bayan Alkali ya gama rubutu sai ya karanta wa Hamisu cewa Kotu ta zartar da hukuncin daurin Wata takwas a gidan yari ko ya biya taran N15,000.

To jama'a,yau adalci ya tabbata,Kotu ce ta yanke hukunci akan Hamisu bayan ya amsa laifin sa ba tare da ba Kotu wahala ba.Ya tabbata kenan cewa ba kazafi aka yi wa Hamisu ba.Ba zai yiwu mutum mai hankali ya amsa laifin da aka yi mashi kazafi da shi ba musamman idan ya sami dama irin ta bayyana a gaban Alkali.
Tun farko da lamarin bai kai haka ba,amma da yake akwai wasu daliban Shaitan da Manzannin Ubayyu, bata gari makiya gaskiya da tsabtataccen tsari,su suka rura wutan wannan batanci irin na kananan Mutane wai kazafi ne akayi wa Hamisu.

Isyaku Garba-Birnin Kebbi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN