Hukumar Alhazan Najeriya Ta Fito da Sabbin Tsare-tsaren Zuwa Haji


Cikin sabbin tsare-tsaren babu wanda za'a bari ya tafi aikin haji sai ya samu mai tsaya masa ya kuma sa hannu cikin takardar neaman zuwa hajin.

Ana bukatar duk mai niya ya samu mai-unguwa ko wani babban jami'in gwamnati dake kan albashi na 14 ko fiye ya tsaya masa.

Baicn wannan hukumar tayi sabon tsarin bada kudin guzuri ga alhazan. A sabon tsarin hukumar alhazan ke da alhakin baiwa alhazan kudaden guzurinsu ta hanyar bankuna maimakon yadda ake yi da inda jihohi ke bayarwa.

Matakin samun wanda zai tsayawa maniyyaci zai taimaka wajen rage yawan masu batawa kasar Najeriya suna, inji kakakin hukumar Alhaji Uba Malam.

Alhaji Uba yace duk wanda zai tsayawa mutum dole ya tabbatar mutumin kwarai ne, nagari wanda ba zai aikata aikin asha ba ya batawa kasa suna. Shi ya sa hukumar ta bada shawara duk wanda zai tafi aikin haji a tabbatar mutum ne nagari.

Hukumomin jin dadin alhazai na jihohin Najeriya sun ce sun dauki matakin ganin an ci nasarar gudanar da sabbin tsare-tsaren kamar yadda shugaban hukumar alhazan jihar Neja Alhaji Adamu Cabi ya bayyana. Yace sun riga sun raba takardun neman tafiya kuma da zara sun ga sa hannu hakimi ko jami'in gwamnati wanda yake kan albashi akalla mataki na 14 sai su amince.

Masanin harkokin aikin haji kuma sakataren kungiyar IZALA reshen jihar Neja Alhaji Aminu Kagara yace sun yi maraba da sabbin tsare-tsaren. Yace sabbin matakan zasu yi maganin matsalolin da aka fuskanta can baya.

Ko baicin kama alhazan jihar Kwara da tarin kwaya a shekarar bara a can Saudiya bayanai sun nuna cewa kimanin alhazan Najeriya 396 ne suka makale a kasar Saudiyan bayan kamala aikin haji.
VOA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN