• Labaran yau

  February 25, 2017

  Haboob,Hadarin guguwar yashi

  A duk lokacin da aka ga wannan irin hadari,dole hankali ya tashi,zukata su tsorata,fargaba da rudani ya bayyana ga duk wanda hadarin ya rutsa da shi.Wannan irin hadarin guguwar yashi ana kiran shi Haboob a Khartoun babban birnin  kasar Sudan.

  Yakan faru ne idan rana tayi zafi kuma yanayi ya zafafa saboda sauke nauyi da ke sararin samaniya irin wannan hadarin yakan faru,a yayin da hadarin ke tafe yana lakume duk abin da ya samu a bisa hanyar sa,yakan canja yanayin kasa a cikin awowi kadan,yakan bizine wasu abubuwa da ya rutsa da su kuma ya shafe su daga doron kasa tamkar babu su a da.

  Isyaku Garba-Birnin kebbi
  @ISYAKUWEB
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Haboob,Hadarin guguwar yashi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama