• Labaran yau

  February 27, 2017

  Argungu- An yi Addu'a wa Buhari wajen saukan Alkur'ani

  Dalibai a Argungu Sunyi yi wa Shugaba Muhammadu Buhari Addu'a wajen Bukin Saukar Karatun Al' Qurani.
  Matar Gwamnan jihar Kebbi Haj. Dr. Zainab Abubakar Atiku Bagudu da tawagan matan sun hallice bukin saukar karatun Al'Qurani Maigirma a garin Argungu da ke jihar wanda wasu dalibai suka yi a makarantar USMAN BIN AFFAN da ke unguwar lowcost a garin na Argungun jihar Kebbi.
  Wanan makarata ita ce wanda uwargidan shugaban kasa Maigirma Hajiya Aishatu Buhari ta kaddamar da kuma take kula da yaran. 

  Malamai, Dalibai da Mata sunyi anfani da wanan daman sun yi ma shugaban kasa addu'ar dawowa lafiya daga kasar waje inda ya je domin karin neman lafiya.
  Wani abin farin ciki a nan har da makauniya mai suna Hajaru Muhammed da makaho Dankasimu Sani cikin wadanda suka sauke Al'Qurani Maigirma a makarantar.

  Dr Zainab tayi godiya da adduan da akayi kuma ta yaba ma yaran da sukayi sauka.
  Cikin mallami da suka halarci taro akwai Malam Nasiru Mera Argungu,
  Da kuma Kantoman Argungu Alh Mu
  sa Tungulawa.

  Sabatu Andrew-BirninKebbi
  @isyakuweb Ku biyo mu a Facebook
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Argungu- An yi Addu'a wa Buhari wajen saukan Alkur'ani Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama