An kona 'Yan Fashi da ran su a Calabar

A garin Calabar an kona wasu matasa biyu da ake zargi da hannu wajen aikata fashi da makami.Bayanai sun nuna cewa daya daga cikin 'yan fashin an kona shi ne a anguwan White house,shi kuma dayan an kona shi ne a Abua kusa da anguwan Ephriam da ke cikin garin na calabar.

'Yan fashin dai suna cikin gungun 'yan fashi da yawan su ya kai akalla 30 rike da miyagun bindigogi da makamai suna tafe suna fashi da rana tsaka a cikin garin na Calabar,a cikin wannan yanayi ne 'yan sanda suka yi artagu da gungun 'yan fashin wanda yayi sanadin tarwatsewar gungun 'yan fashin bayan an yi musanyar wuta ta hanyar harbi da bindigogi tsakanin 'yan fashin da 'yan sanda.

Wasu daga cikin su an kashe su,kana wasu kuma suka gudu,wasu kuma masu ranukkan bindiga a jikin su kuma sun yi kokarin tserewa amma mutanen gari suka afka masu da duka kuma aka kona su.
An kona 'Yan Fashi da ran su a Calabar An kona 'Yan Fashi da ran su a Calabar Reviewed by on February 16, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.