Allah Ya yiwa Shugaban DSS a Kano rasuwa


Allah ya yiwa shugaban Hukumar tsaro ta farin kaya a jihar Kano Abdullahi Chiranci rasuwa

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar 4 ga watan Fabarairu a Asibiti Malam Aminu Kano, a cewar jaridar Daily Nigerian mai buga labaranta a Intanet.

Jaridar ta kuma ce, an garzaya da marigayin ne zuwa asibitin bayan yan kamu da ciwon cikin da ya sa aka garzaya da shi asibitin.

Sannan ta ci gaba da cewa, za a kai gawarsa mahaifarsa garin Chiranchi a jihar Katsina a inda a can za a yi jana'izarsa a yau.

Aiko da ra'ayinka dangane da wannan
Naij.com
Allah Ya yiwa Shugaban DSS a Kano rasuwa Allah Ya yiwa Shugaban DSS a Kano rasuwa Reviewed by on February 06, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.