• Labaran yau

  February 08, 2017

  Aisha,Macen da ke farautar 'yan Boko Haram


  Wani labari da naij.com ta ruwaito ya nuna cewa Aisha  Bakari Gombi wata Mace ce mai farautar 'yan kungiyar boko haram, jaruntar wannan Macen ya sa ana kiran ta "Sarauniyar Mafarauta".Aisha haifaffar kauyen Duggu ce wanda tafiyar minti 30 ne daga kauyen Chibok,inda 'yan boko haram suka sace 'yan Makarantar  mata shekarar 2014.
  Aikwai dubban Masu farauta da Hukumar Sojin Najeriya ta dauka aikin sintirin wucin gadi,amma Aisha tana daya daga cikin Mata kalilan da sukace jajirce da wannan sintirin farautar 'yan kungiyar boko haram din.Duk da yake Aisha Musulma ce amma ita da sauran masu farautar sukan yi amfani da wasu tsari na gargajiya domin kare kan su daga albarush i kafin su tsunduma a cikin daji.Asha 'yar shekara 38,tana jagorantar runduna ce ta Mafarauta 'yan tsakanin shekaru 15-30 kuma sukan yi magana ne ta hanyar amfani da sauti irin na dabbobi ko tsuntsaye.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Aisha,Macen da ke farautar 'yan Boko Haram Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama