Afrika ta kudu - 'Yan Najeriya sun dauki Makamai

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Afrika ta kudu sun nuna cewa a ranar Juma'a 24/2/2017 da ta wuce ne aka yi mummunar arangama tsakanin wasu 'yan Najeriya mazauna Arika ta kudu da wasu matasa masu kyamar baki a cikin kasar.Rahoton ya nuna cewa 'yan Najeriya sun ki su sheka a yayin da matasan suka nufato su,su kuma 'yan Najeriya suka dauki makamai domin su kare kan su.

Idan baku manta ba a can  baya,'yan Najeriya sun fuskanci wulakanci bayan an lakada wa wasu a cikin su dukar tsiya tare da kona shagunan su.Rahotun ya nuna cewa rigimar ya fi kamari ne a birnin Pretoria da ke kasar ta Afrika ta kudu.

Isyaku Garba-Birnin Kebbi
@ISYAKUWEB
Afrika ta kudu - 'Yan Najeriya sun dauki Makamai Afrika ta kudu - 'Yan Najeriya sun dauki Makamai Reviewed by on February 25, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.