Zaharaddeen Sani ya musanta zargin neman maza

Zaharaddeen Sani da Rahma Sadau da kuma sauran abokan aiki
Daya daga cikin jaruman da finafinan Hausa da taurararonsu ke haskawa Zaharaddeen Sani, ya musanta zargin da ake yi masa da neman maza.
A hirarsa da jaridar Premium Times mai yada labarai a yanar gizo a ranar Lahadi 28 ga watan Janairu shekarar 2017, matashin dan asalin Jihar Kaduna ya bayyana wannan zargin da cewa, zuki tamalle ne da kuma neman bata masa suna.
A hirar, jarumin finafinan ya bayyana cewa, yana da mata da 'ya 'ya biyu Maryam da Mannuira, ya sannan ya kuma bayyana aniyarsa na karin wani auren da wata jaruma a Kannywood wacce ya dade yana so, sai dai har yanzu ba ta amince ba.

Zaharadden wanda ya yi fice a fitowar da ya ke yi matsayin matashin takadari, ya kuma bayyana dangartakarsa da Adam A Zango wanda ya ce a da, ba sa ga maciji har ta kai ga ba ya yarda su fito a fim daya, ko kuma a wata alaka a waje, ya ce yanzu wannan ta kau.
Ya kuma ci gaba da bayyana alkarsa da sauran jarumai maza da mata irinsu Ali Nuhu da Jamila Umar da sauransu da cewa kyakkyawa ne.
Jarumin ya bayyana matakin korar da kungiyar masu shirya finafinai ta MOPPAN ta yiwa Rahma Sadau da cewa ya yi daidai, sannan kuma ya ce idan za a rinka yanke hukunci na ba sani ba sabo ga wanda ya karya doka to za a gyara sana'ar.
Baya ga sana'ar fitowa a finafinai a cewarsa, ya na sana'ar sayar da motoci domin shi ma'abocin motocin kawa ne.
An dai sha zargin fitattun jarumai masu shirya finafinai da badala a ciki da wajen sana'arsu ta shirin fim, hakan ya sa suka sa wando daya da Hukumar tace finafinai da dab'i ta jihar Kano musamman a lokacin mulkin Ibrahim Shekarau.
Har ta kai a shekarar 2016 Adam A. Zango ya rantse da Al kur'ani tare da dora shi a kansa a cikin wani shirin talbijin a yayin hira da shi, don ya wanke kansa daga zargin neman maza.
NAIJ.COM HAUSA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN