'YAN MATAN CHIBOK DA AKA CETO SUN FARA TEREREN BANKADA GAME DA GASKIYAR MASU DAUKAR NAUYIN BOKO HARAM

Wani limamin majami’a, Fasto Bulus Buba da ke kauyen Chibok ya bayyana cewa komowar wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a ranar 14 ga wata Afrilun, 2014 ya fara bayyana gaskiyar su wa ke da hannu wajen daukar nauyin mayakan na Boko Haram.
‘Yan matan na Chibok da gwamnati ta anso daga mayakan Boko Haram ta hanyar cika sharuddan wata yarjejeniya tsakanin kungiyar da gwamnati dai sun bayyanawa ‘yan uwa da iyayensu bayan da gwamnati ta mika su gidajensu don gudanar da bikin Kirismeti yadda ta kasance da su bayan an sace su
Fasto Bulus a yayin da ya ke zantawa da jaridar Daily Post a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno a yau Laraba, ya bayyana cewa tattaunawarsa da wasu daga cikin ‘yan matan da aka karbo daga hannun Boko haram ya nuna cewa akwai hannun ‘yan siyasa dumu-dumu a cikin sace ‘yan matan, domin dai sai da ‘yan matan suka shafe sama da watanni biyu a wani GRA da ke cikin babban Birnin Maiduguri kafin daga baya kuma a dauke su zuwa karamar hukumar Gwoza
Fasto Bulus ya ci gaba da cewa “‘Yan matan sun ce sun shafe watanni 8 a Gwoza tare da wasu matan da mayakan suka sace. Kuma an ajiye su ne gidan wani babban dan siyasa a karamar hukumar ta Gwoza har zuwa lokacin da wani jirgin yaki ya jefo bom kan gidan inda ya yi sanadiyyar kashe wasu daga cikin ‘yan matan”
Ya ci gaba da cewa “Daga bisani ne aka dauke ‘yan matan aka yi dajin Sambisa da su, sannan kuma aka rarraba su rukuni rukuni ga rundunoni daban-daban na mayakan.”
Wasu daga cikin rundunonin sun aurar da ‘yan mata ta dole ga mayakansu da kwamandojinsu a yayin da wasu ‘yan matan kuma suka fuskanci fyade daga mayakan a duk lokacin da suka bukace su.

(Al'ummata)

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN