Yahya Jamme ya sauka daga mulki, ya kuma tafi gudun hijira

Tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jamme ya sauka daga muki kuma ya je gudun hijira.Ana sa ran zai bi Shugaba Alpha Conde na kasar Guinea inda zai fara sabuwar rayuwa bayan shugabanci.
Wannan ya biyo bayan namjin kokari da shugabannin Africa suka yi ne na dinke barakar da ke tsakanin Jamme da sabon shugaban na Gambia karkashin jagorancin shugaba Alpha Conde na Guinea da shugaba Mohamed Qoud Abdel-azeez na kasar Mauritania.
Kalli bidiyon jawabin ban kwana na karshe a matsayin sa na shugaban kasa kafin ya sauka a mulki.A cikin bidiyon yayi bayani cewa baya son ya dauki alhaki akan ko wani rai da zai iya salwanta,ko jinin dan Gambiya da zai iya zuba sanadin rikicin zaben kasar.Ya kuma kara bayani cewa Allah kadai ne wanda ya iya adalci kuma a bisa wannan dalilin ya mai da al'amarin shi ga Allah (SWA).

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN