Wata 'yar kunar-bakin-wake ta rungumi mutum a Maiduguri

A kalla mutane uku ne aka kashe a wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kai da safiyar Larabaa Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Wannan dai na zuwa ne kimanin makwanni biyu da kai hari jami'ar Maidugurin, inda mutane hudu suka rasa rayukansu ciki har da wani Farfesa.
Wani jami'in bayar da agaji ya shaida wa BBC cewar macen farko yt yi hakon gidan wani dan banga ne wanda aka sani da yin bincike a kan motoci a manyan hanyoyin garin.
Sai 'yar kunar bakin waken ta kwankwasa kofar gidan dan bangar, wanda rahotannin suka ce ya ki bude kofar.
Saboda haka sai ta yi maza ta rungumi wani mutum da ke kan hanyarsa ta zauwa masallaci kuma ta tayar da bam din da ta yi damara da shi.
Dukkansu biyu sun mutu a harin.
Amma mutumin da ya kai hari na biyun bai samu ya kai ga babban masallacin anguwar Kaleri ba saboda an hanashi zuwa wurin.
Ya mutu shi kadai tare da raunata mutane biyu.
BBCHausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN