WASU ABUBUWAN DA YA KAMATA KU SANI GAME DA DUTSEN UHUDU

WASU MUHIMMAN ABUBUWA GAME DA DUTSEN UHUD

Daga Malam Aminu Daurawa

Manzon Allah SAW ya ce: Hakika Dutsen Uhud yana sonmu, mu ma muna sonsa, Bukhari.

Wata rana Manzon Allah SAW yana kan Dutsen Uhud, sai Dutsen ya yi girgiza, sai Manzon Allah saw yace: Ka tabbata ya Uhud, akan ka akwai Annabi saw, Da Siddiqu (Abubakar), da Shahidai guda biyu, (Umar da Usman).

Wannan Dutse yana Arewa da Madina, kusan tsawon Kilomita hudu daga Masallacin Annabi saw, tsawonsa ya kai kilo bakwai, fadinsa kilo hudu.

Duk sanda naje jikin wannan Dutsen abu hudu nake tunawa,

1- Manyan Sahabbai 70 da suka yi shahada wajan kare addinin Allah a wannan waje

2- gumurzun da akayi a wannan waje tsakanin karya da gaskiya, mutum dari bakwai suka tunkari dubu uku

3- wannan waje aka jiwa Annabi saw rauni, har jini ya zuba, saw.

4-  wannan gurin tarihi ne na mazan jiya, daya kamata mu yi koyi da su wajen taimakon addini da rayukan mu, da kudin mu, da lokacin mu, Allah ka bamu ikon yada addini da kareshi, da duk damar da muka samu.

WASU ABUBUWAN DA YA KAMATA KU SANI GAME DA DUTSEN UHUDU WASU ABUBUWAN DA YA KAMATA KU SANI GAME DA DUTSEN UHUDU Reviewed by on January 11, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.