SHARUKH KHAN YA GINDAYA DOKOKI GA DUK SAURAYIN DA KE SON DIYAR SA

Shahararren Jarumin nan na Bollywood, Shah Rukh Khan ya gindaya wasu dokoki ga duk saurayin da zai ce ya na son ‘yar sa Suhana mai shekaru 16.
Jarumin wanda uba ne ga ‘yaya uku; Aryan Suhana da Abram, ya bayyana cewa yana matukar son ‘yayan nasa kuma yana sanya masu ido ya kula da su yadda ya kamata.
A wata Hira da ya yi, jarumin ya bayyana cewa duk saurarin da zai ce yana son ‘yar sa to sai ya:
  1. Kasance ya na da aikin yi
  2. Fahimci cewa shi Sharukh Khan baya son shi
  3. Ya samo lauya mai tsaya masa
  4. Ya sani cewa Suhana Gimbiyar Shahrukhan ce, ba wata kyauta ba da ya ciwo
  5. Ya sani cewa shi Sharukh Khan ba ya tsoron komawa gidan yari
  6. Ya sani cewa duk abunda ya yi wa yarsa sai ya rama mata.
Jarumin dama dai ya dade yana sanya ido akan irin samarin da ke kusantar ‘yar ta sa, kuma da alama ya yi wannan magana ne domin ya razana su.
SHARUKH KHAN YA GINDAYA DOKOKI GA DUK SAURAYIN DA KE SON DIYAR SA SHARUKH KHAN YA GINDAYA DOKOKI GA DUK SAURAYIN DA KE SON DIYAR SA Reviewed by on January 15, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.