Mayakan Boko Haram Sun Kai Wa Wasu Daliban Jami’ar Maiduguri Farmaki

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai wa wasu matafiya a cikin mota farmaki akan hanyar su ta zuwa jahar Taraba daga Maiduguri.
Motar na dauke ne da wasu daliban jami’ar Maiduguri da ke kan hanyarsu ta zuwa gida bayan da suka kammala jarrabawarsu tare da wasu mutanen daban.
Mayakan sun farwa motar, inda suka bude mata wuta suka kuma kashe mutane da dama yayin da yawa suka jikkata. Wasu kuma sun samu nasarar tserewa bayan da direban ya tsayar da motar.

Wani malamin jami’ar Maiduguri ya shaidawa Kafar yada Labarai na BBC cewa sun tabbatar da mutuwar dalibai biyu daga ciki, yayin da wasu uku kuma suna babban asibitin koyarwa na Maiduguri.
Baya ga daliban jami’ar, akwai kuma wasu mutane da suka mutu wadanda ba a san adadinsu ba zuwa yanzu.
Makonnin biyun da suka gabata ne kungiyar ta Boko Haram ta kai harin ta na farko a jami’ar ta Maiduguri inda mutane biyar suka rasa rayukan su,a ciki har da wani farfesa.
ALUMMATA
Mayakan Boko Haram Sun Kai Wa Wasu Daliban Jami’ar Maiduguri Farmaki Mayakan Boko Haram Sun Kai Wa Wasu Daliban Jami’ar Maiduguri Farmaki Reviewed by on January 29, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.