MADARAR KYANKYASU CIKE TAKE DA SINADARAN KARINLAFIYA - BINCIKE YA GANO

Masu binciken kimiyya sun gano cewa madarar da kyankyasu ke ciyar da ‘yayansu da shi na kunshe da sinadaran karin lafiya, kafar yada labarai ta CNN ta rahoto.
An yi binciken ne akan kirar Kyankyaso mai suna ‘Pacific Beetle Cockroach’ a turance wanda ke iya haifar ‘yaya kai tsaye ba tare da yin kwai ba.
Daya daga cikin masu binciken Leonard Chavas ya bayyana cewa abincin da kyankyasun ke ciyar da ‘yayansu ba kamar madarar da muka sani ba ne, yace ta kyankyasun na kunshe da ninki uku na sinadaran kara karfin jiki (Energy) da ke cikin madarar Bauna da kuma ninki hudu na sinadarin da ke cikin madarar shanu.

Chavas wanda ya ce ya dandana madarar sau daya, ya ce ana samun shi ne a tsakiyar cikin kyankyason. Ya kuma ce, a sakamakon yanayin da ake tatsar madarar, ba za’a iya samaun adadin da za’a iya ciyar da mutanen duniya ba, don haka suna kokarin ganin cewa sun fahimci madarar sosai yadda zasu iya samar da ita da yawa.
AL'UMMATA
MADARAR KYANKYASU CIKE TAKE DA SINADARAN KARINLAFIYA - BINCIKE YA GANO MADARAR KYANKYASU CIKE TAKE DA SINADARAN KARINLAFIYA - BINCIKE YA GANO Reviewed by on January 09, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.