KOTUN KOLI TA SAKE BUDE SHARA'AR MANJO AL-MUSTAPHA

Kotun koli ta baiwa Gwamnatin jahar Lagos damar sake bude Shari’ar tsohon dogarin margayi Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha mai murabus, game da zargin kisan mai dakin margayi Abiola, Alhaja Kudirat Abiola.
Gwamnatin jahar Lagos din dai ta shigar da bukata a kotu na neman a bata dama ta kalubalanci hukuncin da babban kotun tarayya ta yanke a 2013 bayan da ta kori Shari’ar ta Manjo Al-Mustapha, tare da sallamar shi.
Ita dai Alhaja Kudirat an kashe ta ne a ranar 4 ga watan Yuni, shekarar 1996, an kuma gurfanar da Al-Mustapha a bisa tuhumar kisan a ranar 22 ga watan Oktoba 1998.
Laifukan da aka tuhumi Al-Mustapha sun hada da kwashe kudaden marigayi Janar Sani Abacha, da yunkurin juyin mulki, da kuma kashe Hajiya Kudirat Abiola.
An dai yi ta fafatawa a shari’ar wacce ta shafe tsahon shekaru 14. Sannu a hankali aka kori dukkanin kararrakin, banda na kisan Kudirat.
A watan Junairun 2012, kotu da ke jahar Lagos ta yanke wa Al-Mustapha da Mr. Lateef Shofolahan hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Sai dai wadanda aka yankewa hukuncin ba su yarda da shi ba, inda suka daukaka kara. Bayan nan ne a ranar 12 ga watan Yuni 2013 aka kammala shari’ar, kotu ta sallami Al-Mustapha.
Manjo Hamza Al-Mustapha dai shi ne ya rike mukamin shugaban masu tsaron marigayi tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya, Janar Sani Abacha.
(Al'ummata)

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN