• Labaran yau

  January 21, 2017

  KO DONALD TRUMP ZAI GOYI BAYAN KAFA KASAR BIAFRA ?

  Tun dai bayan zaben shugaba Muhammadu Buhari a bara, dangantakar Najeriya da Amurka ta dan inganta.
  Dangantakar dai ta yi tsami ne bayan zargin cin zarafin bila'dama da ake yiwa sojojin Najeriyar, musamman ma a yakin da suke yi da mayakan Boko Haram.
  Sojojin Najeriyar suna samun horo da kuma kayan aiki daga gwamnatin Barack Obama, don haka za su so Mista Trump ya ci gaba da karfafa wannan dangantakar.
  Najeriya za ta kuma so ta samu kyautatuwar dangantakar kasuwanci da Amurkar.
  Wasu daga cikin manyan kamfanonin Amurka na cikin gaggan masu zuba jari a bangaren makamashi a Najeriya, amma kuma gano danyan man da Amurkar ta yi ya sa yawan man da ta ke saya daga kasar ya ragu.

  RFI Hausa
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: KO DONALD TRUMP ZAI GOYI BAYAN KAFA KASAR BIAFRA ? Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama