DUBBAN JAMA'A NA GUDANAR DA TATTAKI A BIRNIN WASHIGTON

Ana sa ran akalla mutane 200,000 su shiga cikin tattakin da dubban mata suka shirya gudanarwa a birnin Washington na Amurka.
Wadanda suka shirya tattakin sun ce, suna son janyo hankalin Duniya game da halin da mata ke fuskanta na rashin daidaiton jinsi, da kuma nuna wariyar launin fata, wadanda suke fargabar kara tabarbarewarsu karkashin gwamnatin Trump.
Tuni dai dubban mutane ciki har da Amurkawa suka fara fantsama cikin titunan birane da dama a kasashen New Zealand da Australia, don nuna goyon bayansu kan tattakin da dubban mata suka shirya yi a birnin Washington.
Ana sa ran gudanar ta tattakin na dubban jama’a a baki dayan jihohin kasar Amurka, da kuma kasashen Duniya akalla 50.

BBCHausa
DUBBAN JAMA'A NA GUDANAR DA TATTAKI A BIRNIN WASHIGTON DUBBAN JAMA'A NA GUDANAR DA TATTAKI A BIRNIN WASHIGTON Reviewed by on January 21, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.