DANGOTE YA KAFA KAMFANIN KERA MANYAN MOTOCI A NAJERIYA


Shahararren dan kasuwannan kuma wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika Aliko Dangote ya kafa wata sabuwar kamfanin kera manyan Motoci a kasa Najeriya.

An kafa kamfanin ne a jihar Legas.

Dangote yace kamfanin zata dinga kera akalla manyan motoci 10,000 duk shekara.

Wani mai Magana da yawun kamfanin, ya sanar da cewa kamfanin sun hada hannu ne da wata kamfanin kera motoci dake kasar China domin samun nasara akan hakan.

Dangote ya na shirin kaddamar da sabuwar kamfanin matatar man sa da na yin takin zamani a shekara ta 2017.

Daga karshe yace dole ne a hana karfi da karfe domin ganin an kafa kamfanoni a kasa Najeriya domi samun kudaden shiga.

Premium Times Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN