Daga karshe: Jammeh ya fice daga Gambia zuwa Guinea

Tsohon Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya fice daga kasar bayan ya amince ya mika mulki ga Adama Barrow, wanda ya ka da shi a zaben shugaban kasa na watan jiya.
Da tsakar daren ranar Assabar ne Alhaji Jammeh ya sanar da cewa zai sauka daga kan mulki bayan kwashe shekaru 22 yana mulkin kasar.
Ya dai bar kasar cikin wani karamin jirgin sama a filin jirgin birnin Banjul tare da matarsa da kuma shugaban kasar Guinea Alpha Conde.
Ana tunanin tsohon shugaban zai fara sauka a Guinea din ne kafin ya nemi mafaka a wata kasar daban.
Kungiyar Ecowas ta ce daga kasar ta Guinea zai je Equatorial Guinea ne.

Bankwana

Wakilin BBC dake birnin Banjul yanzu haka Alaistair Leithead ya ce:
Tsohon shugaban kasar Jammeh ya iso filin jirgin saman Banjul ne a cikin wani jerin gwanon motoci.
Bayan da ya fito ya tsaya ya saurari kidan 'yan badujala na sojojin kasar a karo na karshe sannan ya juya yana tafiya kan wata jar darduma zuwa cikin wani karamin jirgi da ba ya da rubutu a jikinsa.
Daga nan sai ya taka tsanin shiga jirgin sannan ya juyo ya dagawa taron jama'ar da suka rako shi hannu kuma ya sumbaci alkur'aninsa kafin ya shige cikin jirgin.
Muhimman mutane da yawa da kuma magoya bayansa da suka yi dafifi a wajen filin jirgin sun shiga wani hali na bacin rai bayan ganin shugabansu ya tafi bayan kwashe shekaru 22 kan mulki.
Sai dai kuma wasu da yawa a cikin kasar ta Gambia sun yi murna da ganin karshen abin da suke ganin mulkin kama-karya ne wanda bai mutunta hakkin bil'adama da kuma 'yancin fadin albarkacin baki sai can ba a rasa ba.

BBCHausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN