'Ba za mu yi wa MTN kora da hali daga Nigeria ba'

Ministan sadarwa na Najeriya Adebayo Shittu, ya ce bai kamata gwamnatin kasar ta yi wa Kamfanin sadarwa na MTN kora da hali ba, a yayin da 'yan majalisar dokoki ke gudanar da bincike kan zargin cewa kamfanin ya fitar da wasu kudade ba bisa ka'ida ba, watanni uku kacal bayan da gwamnatin kasar ta ci tarar kamfanin fiye da dala biliyan daya.
Jawabin Mista Adebayo Shittu shi ne na farko da gwamnati ta yi a kan bincike na baya-bayan nan da ake yi wa MTN, inda ya ce gwamnatin ba za ta so ganin an yanke wa kamfanin hukunci mai tsanani ba, a kasar da kamfanin ke cin kasuwarsa sosai, idan har aka tabbatar da gaskiyar zargin.''Ba wanda zai ce MTN ba shi da muhimmanci a Najeriya - dole mu karfafa musu gwiwa, bai kamata mu kore su ba,'' a cewar Mista Shittu, a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
MTN, shi ne kamfanin wayar salula mafi girma a Najeriya, inda ya yi barazanar janyewa daga kasar a shekarar 2016, sakamakon wani takun saka da ya yi da gwamanti saboda rashin yin rajistar wasu layukan waya, inda daga bisani gwamnati ta rage yawan tarar da ta ci kamfanin da kusan kashi 70.
Hakan ne yasa tarar ta dawo dala biliyan daya.
Ministan sufurin ya kuma ce, ''Ana zaton cewa basu yi laifi ba kuma muna addu'a ya kasance hakan, dole ne su saura."
Jawabinsa ya yi daidai da abin da ya fada a lokacin da aka ci MTN tarar dala biliyan 5.2 a shekara 2015 - kudin da yake daidai da ribar da kamfanin yake samu cikin shekara biyu a Najeriya - saboda kasa yi wa layukan wayoyi rijista.

'Sabuwar barazana'
A yanzu kamfanin yana fuskantar wani babban hukuncin idan har binciken da majalisar dattawan kasar ke yi ya samu hujjar cewa kamfanin MTN ya fitar da kudi kimanin dala biliyan 13.9 daga kasar tsakanin shekarar 2006 zuwa 2016, kamar yadda ake zargi.
Sai dai MTN ya ce bai karya dokar hada-hadar kudi ta Najeriya ba.

BBCHausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN