An Zarcewa Arewa Maso Gabashin Najeriya Da Shekaru 500 ta Fannin Ilmi- Inji Farfesa Njodi

Shugaban Jami'ar Maiduguri dake Arewaci Najeriya Farfesa Abubakar Njodi ya ce rikicin kungiyar Boko Haram ya maida yankin na Arewa maso gabashin Najeriya baya ta fannin ilmi da  shekaru 500.
Farfesa  Njodi ya yi nuni da cewa tun kafin  bullar kungiyar Boko Haram akwai masana dake ganin an bar yankin a baya da kamar shekaru 150 ta fannin ilmi bisa sauran sassan kasar musamman kudanci, sai gashi kuma an sami wannan bala'i.
Ya shaidawa tawagar komitin Asusun tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya cutar da suka ziyarce shi a Maiduguri, don jajanta masa sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai jami'ar da yayi sanadiyyar mutuwar ma'aikata uku, cewa ta fannin ilmi dai yankin na bukatar jama'a su mike sosai a tallafa.
RFI Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN