An Yiwa Ofishin ‘Yan Sandan Garin Dangi Fashi a Jihar Filato


Al’ummar garin Dangi sun bayyana fargabarsu ga abin da ka iya biyo baya, bayan da aka kashe ‘dan sanda tare da kwasar makamai daga ofishin ‘yan sandan garin.
Muryar Amurka tayi kokarin tuntubar jami’an ‘yan sandan jihar Filato don jin bayanai ya ci tura, inda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Terna Tyopev, ke cewa bai sami cikakken bayanai kan lamarin ba.
Sai dai kuma wasu mazauna garin da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta zanta da su sun bayyana cewa, da missalin karfe biyu na dare mutanen suka kaiwa ofishin ‘yan sandan hari suka kwashe makamai tare da kashe wani jami’i guda ‘daya.
Yanzu haka dai komai na tafiya yadda ya kamata a garin Dangi, duk da yake akwai zaman fargabar abin da ka iya faruwa.
Domin karin bayani ga rahotan Zainab Babaji.
voa hausa
An Yiwa Ofishin ‘Yan Sandan Garin Dangi Fashi a Jihar Filato An Yiwa Ofishin ‘Yan Sandan Garin Dangi Fashi a Jihar Filato Reviewed by on January 24, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.